IQNA

Sarkin Saudiyya Ya Kori Babban Mai Kula Da Lamurran Ofishinsa

21:14 - October 03, 2021
Lambar Labari: 3486380
Tehran (IQNA) sarkin Saudiyya ya kori babban mataimakinsa kan lamurran gudanarwa na ofishinsa.

Kamfanin dillancin labaran WAS na kasar Saudiyya ya bayar da rahoton cewa, a yau sarkin Saudiyya Salman Bin Abdulaziz ya kori babban mataimakinsa kan lamurran gudanarwa na ofishinsa.

Rahoton ya ce sarkin Saudiyya Salman Bin Abdulaziz ya kori naser Bin Abdulrazzaq Bin Yusuf Alnafisi babban mataimakinsa kan lamurran gudanarwa na ofishinsa daga kan mukaminsa, ba tare da bayyana dalilin hakan ba.

Bayan korarsa, an nada Abdulaziz bin Ibrahim Bin Hamad Alfaisal a kan mukamin nasa, wanda yake a matsayin minista mai kula da lamurran Khadimul Haramain.

 

4001975

 

captcha