IQNA

Isra'ila Ta Ce Tana Shirin Sake Kulla Alaka Da Wasu Kasashe

18:09 - October 06, 2021
Lambar Labari: 3486392
Tehran (IQNA) ministan harkokin wajen Isra'ila ya bayyana cewa, suna kokarin ganin sun sake kulla alaka da wasu kasashe.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, Yair Lapid ministan harkokin wajen gwamnatin yahudawan Isra'ila ya bayyana cewa, suna kokarin ganin sun sake kulla alaka da wasu kasashe.

Lpid ya ce, a halin yanzu akwai wasu daga cikin kasashe wadanda suka bayyana sha'awar kulla alaka da Isra'ila, wadanda a da basu da wata alaka da ita, inda ya ce Isra'ila za ta yi amfani da wannan damar wajen kulla hulda da su.

Duk da cewa dai Lapid bai ambaci sunayen kasashen ba, amma dai za to mafi karfi wasu ne daga cikin kasashen larabawa.

Bisa matsin lambar gwamnatin Trump, wasu daga cikin kasashen larabawa da suka hada da Hadaddiyar Daular Larabawa, da Morocco, gami da Sudan da kuma Bahrain, sun kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra'ila.

captcha