IQNA

Masu Kare Hakkokin 'Yan Adam Na Zargin Facebook Da Nuna Adawa Ga Al'ummar Falastinu

20:22 - October 09, 2021
Lambar Labari: 3486405
Tehran (IQNA) masu rajin kare hakkin bil adama a duniya suna zargin kamfanin facebook da nuna wariya da adawa ga al'ummar falastinu.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, bisa binciken da masu rajin kare hakkokin 'yan adam suka gudanar, sun iya gano cewa, kamfanin facebook ya share abubuwa da dama da suke da alaka da al'ummar Falastinu, da abubuwa da aka wallafa da suka shafi Quds ko zirin Gaza.

Baya mika koke ga kamfanin kan hakan, mai magana da yawun kamfanin na facebook ya bayyana cewa, an samu kure ne wajen goge sakonni da suka shafi falastinawa, kumaya ce za su gudanar da bincike kan hakan domin gyarawa.

Masu kare hakkin bil adama sun ce tun daga ranar 14 ga watan Satumba da kamfanin ya ce ya kafa wani kwamiti domin bincike kan hakan, har inda yau take ba a kara jin wani bayani ko kuma sakamakon binciken ba.

Tun kafin wannan lokacin dai an jima ana zargin kamfanin na facebook da nuna karkata ga manufofin yahudawa masu zaluntar al'ummar Falastinu.

 

4003489

 

 

 

 

 

captcha