IQNA

Jami'an Tsaron Isra'ila Sun Kame Sheikh Barakat Daraktan Cibiyar Kur'ani Ta Masallacin Quds

14:45 - October 26, 2021
Lambar Labari: 3486476
Tehran (IQNA) jami'an tsaron yahudawan Isra'ila sun kame Sheikh Abdulrahman Barak daraktan cibiyar Kur'ani ta masallacin Quds

Shafin yada labarai na asdaapress.com ya bayar da rahoton cewa, yahudawa sun kama Sheikh Abdul Rahman Barakat a yammacin jiya, bayan da gwamnatin yahudawan sahyoniya ta gayyace shi domin amsa tambayoyi kan ayyukan da yake gudanarwa a masallacin Al-Aqsa.

A cewar wasu majiyoyin leken asiri na gwamnatin sahyuniya, yahudawan sun kama Sheikh Barakat ne bayan sun gayyace shi domin amsa tambayoyi a kan ayyukan cibiyar "Al-Muskubia" da ke kula da lamurra na ayyukan kur'ani a masallacin Quds.
 
An sha kama Sheikh Barakat sau da yawa saboda koyarwa da yake yi farfajiyar "Bab al-Asbat" a cikin masallacin Al-Aqsa da kuma kare wannan masallaci.
 
Har ila yau, an bayyana cewa dakarun mamaya sun kafa shingayen binciken ababen hawa a yankuna daban-daban na garin Salwan dake kudancin masallacin Al-Aqsa, kuma al'ummar birnin Quds sun gudanar da sallar magriba a jiya a gaban makabartar Al-Yusufiyyah domin nuna adawa da ta'asar da 'yan  mamaya suke ci gaba da aikatawa. 
 

 

4008094

 

 
Abubuwan Da Ya Shafa:
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha