
Gwamnatin kasar Saudiya ta bawa jakadan kasar Lebanon a Riyad sa’o’i arba’in da takwas da ya bar kasar, sannan ta bukaci jkadanta da ke Beirut ya dawo gida saboda shawartawa.
Saudiya ta dauki wannan matakin ne bayan da ta bukaci ministan watsa labarai na kasar Lebanon George Kordahi ya nemi afuwar gwamnatin kasar ta Saudiya kan furucinsa inda ya bayyana cewa yakin da Saudiyya take kaddamarwa kan al’ummar kasar Yemen bai dace ba.
Banda haka gwamnatin kasar ta saudiya ta hana a sake shigo da wasu kaya daga kasar Lebanon sai abin da hali yayi.
Sannan ta gargadi yan kasar da su dakatar da tafiye-tafiye zuwa kasar Lebanon.
A makon da ya gabata ne aka watsa wani furuci na ministan watsa labarai na kasar Lebanon George Kordahi ya yi kira ga gwamnatin kasar Saudiya ta kawo karshen yakin da take jagoranta a kan al'ummar kasar Yemen tun shekara ta 2015, wamda kuma ya yi wannan furucin ne tun kafin a nada shi a kan mukamin minista.
Wasu da dama dai suna ganin cewa, Saudiyya ce da kanta ta bankado wannan tsohuwar magana kuma ta mayar da ita abin tayar da jijiyoyin wuya tsakaninta da Lebanon, domin ta kawar da hankulan al’ummomin duniya kan batun tonon sililin da tsohon babban jami’in hukumar leken asirin kasar ta Saudiyya Saad Al-jabri ya yi a makon da ya gabata daga kasar Canada, wanda ya bayyana cewa Muhammad Bin Salman ya yi yunkurin kashe marigayi sarki Abdullah a lokacin yana kan mulki, domin ubansa Salman ya dare kan kujerar sarautar kasar Saudiyya..
Bangarori daban-daban a kasar ta Lebanon masu 'yancin siyasa da kuma lamiri, sun yi tir da Allawadai da wannan matsaya ta gwamnatin Al saud, tare da bayyana hakan a matsayin shigar shugula a cikin harkokin Lebanon, kuma hakan yana matsayin hidima ne ga makiya al'ummar musulmi da na larabawa wato Amurka da yahudawan Isra'ila, wadanda masarautar Al saud ke hankoron ganin ta faranta musu rai ko ta wane hali.