IQNA

Abiy Ahmed Ya Yi Gargadin Cewa An Kama Hanyar Mayar Da Ethiopia Kamar Libya Ko Syria

22:28 - November 03, 2021
Lambar Labari: 3486510
Tehran (IQNA) Firayi ministan Habasha Abiy Ahmed ya zargi kawancen 'yan tawayen da kokarin mayar da Habasha tamkar kasar Libya da Syria

A cikin wata sanarwa da ya fitar wannan Laraba, Abiy ya zargi kawancen 'yan tawayen da kokarin mayar da Habasha tamkar kasar Libya da Syria, yana mai cewa: "Sun shirya ruguza kasar  ba wai su gina ta ba."

Ya kuma bukaci 'yan kasar da su goyi bayan yakin, yana mai cewa: "Nasara kan barazanar da makiyanmu ke yi ba za ta samu ba idan ba a hada kai ba."

A karkashin dokar ta-baci, hukumomi na iya daukar duk wani dan kasa da shekarunsa ya kai ga aikin soji, tare da dakatar da duk wata kafar yada labarai da aka yi imanin cewa tana nuna goyon baya kai tsaye ko a fakaice ga kungiyar tawayen TPLF.

Kungiyar Tawayen Tigray People's Liberation Front (TPLF) da ta shafe shekara guda tana yakar gwamnatin Firaiminista Abiy Ahmed, ta yi ikirarin samun gagarumar nasara a mamaye wasu yankuna a 'yan kwanakin nan, tare da kawayenta na 'yan tawayen Oromo Liberation Army (OLA).

Odaa Tarbii, mai magana da yawun OLA, wanda kuma ya yi ikirarin ci samun ci gaba a baya-bayan nan a Amhara da kuma yankin Oromia da ke kewaye da Addis Ababa, ya ce kungiyarsa ta yi niyyar hambarar da gwamnatin Abiy Ahmed, yana mai cewa korar sa abu ne da sukayi nisa akai.

Kalaman na zuwa ne sa'o'i bayan kasar Habasha ta ayyana dokar ta-baci a fadin kasar a ranar Talata tare da bada umurni ga mazauna birnin Addis Ababa da su shirya don kare matsugunan su.

 

4010469

 

Abubuwan Da Ya Shafa: baya-bayan nan hambarar da
captcha