Shafin Alarabi Jadid ya bayar da rahoton cewa, Majiyoyin kiwon lafiya na soji a lardin Sina ta Arewa a kasar Masar sun bayyana cewa, kungiyar ta'adda ta "Lardin Sinai" mai alaka da kungiyar ta'addanci ta Daesh ta kai hari kan sojojin kasar a yammacin birnin Al-Arish da ke lardin Sina ta Arewa.
A cewar wadannan majiyoyin, harin ta'addancin ya kashe sojojin Masar biyu tare da raunata wasu da dama, kuma an kai gawarwakin wadanda aka kashe zuwa mahaifarsu.
Harin ta'addancin dai shi ne na farko tun bayan da shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi ya bayar da umarnin a dage dokar ta baci a kasar bayan shekaru shida.
Tun a shekara ta 2014, yankuna daban-daban a arewa maso gabashin Masar ake fuskantar hare-hare kan sojoji da 'yan sanda da fararen hula, mafi yawan hare-haren na kungiyar Lardin sinai ce mai alaka da Daesh.
Tun a watan Fabrairun 2018 ne dakarun hadin gwiwa na sojojin kasar Masar da 'yan sandan kasar suka kaddamar da wani gagarumin farmakin soji mai suna "Sinai 2018" domin kawar da 'yan ta'adda a yankin na Sinai.