IQNA

Matashi Makaho Dalibin Jami'a Kwararre A Tilawar Kur'ani Mai Tsarki

20:11 - November 07, 2021
Lambar Labari: 3486524
Tehran (IQNA) “Osman Ihab Abdul Karim” matashin dalibi ne a jami’ar Al-Azhar, wanda ​​ya yi fice wajen karatun kur’ani a tsakanin dukkanin takwarorinsa.

Osman Ihab Abdul Karim dalibi ne a shekara ta farko a jami'ar Azhar da ke Masar reshen Usul, wanda ya samu gagarumar nasara a karatun kur'ani.

Ya ce game da rayuwarsa: “An haife ni makaho ne, amma Allah ya yi mani baiwa ta son Alkur’ani, kuma na yi nasara wajen haddace Alkur’ani da kuma iya tilawarsa.

Allah Ta’ala ya albarkace ni da kur’ani fiye da yadda nake fata, kuma ya haskaka idanuna ga Alkur’ani mai girma, ya kuma sanya mani farin jini a wurin mutane saboda kyawun sautin tilawar kur'ani da Allah ya ba ni.

Ya yi nuni da cewa saboda son kur’ani yasa yake saurari radiyon kur’ani na kasar Masar, ya kuma iya yin koyi da manya-manyan malaman kur'ani na Masar irin su Muhammad Siddiq Manshawi, Sheikh Abu al-Ainin al-Shaysha, Sheikh Abdul Basit Abdul Samad. da sauran masu karatu, kuma sun sami ci gaba sosai wajen karatun Alqur'ani.

Wannan dalibi dan kasar Masar makaho kowa ya lura da yadda ya samu ci gaba a karatun kur’ani, har ana gayyatarsa a wurare domin karatun kur’ani. A yanzu haka yana fatan samun damar karatun kur'ani a gidan rediyon Masar.

A cikin wannan faifan bidiyo za a iya sauararen karatunsa aya ta 31 da 32 a cikin surat Baqarah:

 

 

4011178

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: makaho
captcha