IQNA

An kai wani harin bam a wani masallaci a Lardin Nangarhar na kasar Afganistan

20:28 - November 12, 2021
Lambar Labari: 3486549
Tehran (IQNA) Wani harin bam da aka kai a kusa da wani masallaci a lardin Nangarhar da ke gabashin kasar ya kashe mutane akalla hudu tare da jikkata wasu 18 ciki har da limamin masallacin.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya habarta cewa, wani harin bam da aka kai a kusa da wani masallaci a lardin Nangarhar na kasar Afganistan ya kashe mutane akalla hudu tare da jikkata wasu 18.
 
Atal Shinwari, wani mazaunin yankin, ya ce fashewar bam ta faru ne da misalin karfe 1:30 na ranar yau Juma'a.
 
Wani jami’in Taliban da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa akwai yiyuwar hasarar rayuka ya karu amma bai yi karin bayani ba.
 
Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, amma dai ana nuna yatsan tuhuma a kan 'yan ta'addan Daesh wadanda suka saba kai irin wadannan hare-hare.

 

4012546

 

 

 

captcha