Shafin yada labarai an Akhbar Alan ya bayar da rahoton cewa, Khalid Ba Taraf babban kwamandan kungiyar 'yan ta'adda ta Alka'ida a Yemen da jazirar Larabawa ya tabbatar ad cewa suna cikin masu taimakawa Saudiyya wajen yaki da mayakan An sarullah da aka fi sani da Alhuthi a Yemen.
Wannan kasurgumin dan ta'adda ya bayyana hakan ne dangane da yakin da ake yi yanzu haka tsakanin dakarun gwamnatin san'a da mayakan Ansarullah ke mara wa baya, da kuma mayakan Saudiyya da kuma wadanda take marawa baya da suka hada da sojojin haya, da kuam kungiyar 'yan ta'addan takfir da suka hada da alkaida ad Daesh.
Ya ce suna aiki kafada da kafada tare da sojojin Saudiyya wajen yaki da sojojin gwamnatin San'a da kuam mayakan Alhuthi.
Tun kafin wannan lokacin dai Ansarullah sun sha bayyana cewa, mutanen ad suke yaki da su 'yan ta'adda ne, wadanda wasunsu ma an kwaso su ne daga Syria, wadanda suke yi wa Saudiyya yaki a kan al'ummar kasar Yemen a halin yanzu.