IQNA

Babban Taron Rahmatul Lill Alamin A Pakistan

22:59 - November 15, 2021
Lambar Labari: 3486563
Tehran (IQNA) msuulmin Pakistan suna gudanar da taron rahmatul lil alamin

Msuulmin kasar Pakistan suna gudanar da wani zaman taro wanda yake mayar da hankali kan gudunmawar da manzon Allah (SAW) ya bayar wajen shiryar da bil ama.

Mahalarta wannan taro, sun yi ishara da ayoyi masu albarka daga cikin kur'ani mai tsarki, daga cikin ayoyin akwai ayar da ke cewa da manzon Allah (SAW)  “Kuma ba mu aiko ka ba face rahama ga talikai” tare da yin nuni da muhimmancin yin koyi da matsayar ma'aiki a cikin dukkanin lamurra na 'yan adamtaka da jin kai da tausayi irin nasa.
 
Ya zo a cikin ruwayoyi da dama kan cewa, akwai mutanen da suka musulunta saboda kyawawan dabi'u irin na manzon Allah (SAW) ba tare da an yi musu wa'azi ba, domin dabiunsa da halayensa baki dayansu wa'azi ne nasiha ce darasi ne ga dukkanin 'yan adam a cikin rayuwarsu.
 
Sannan kuma taron ya jaddada wajabcin hadin kan al'ummar musulmi a matsayin daya daga cikin abubuwa na wajibi da ke cikin kur'ani da sunnar ma'aiki.
 

 

4013394

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: musulmin Pakistan ، gudunmawa ، manzon allah (saw) ، shirya ، bil adama
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha