Shafin yanar gizo na OIC ya bayar da bayanin cewa, a yau Hussein Ibrahim Taha ya fara aiki a matsayinsa na babban sakataren kungiyar kasashen musulmi a hukumance.
A zaman taro karo na arba'in da bakwai na majalisar ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi, da aka gudanar a Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar, aka ayyana shi a matsayin sabon sakataren janar na kungiyar.
An haifi Hussein Ibrahim Taha a shekarar 1951 a birnin Abshi na kasar Chadi, inda ya yi karatun firamare da sakandare a kasar Chadi.
Baya ga aikin jakadanci da ba da shawara, an zabe shi a matsayin ministan harkokin waje da hadin gwiwar kasa da kasa na kasar Chadi a shekarar 2017, kuma an nada shi mai baiwa shugaban kasa shawara a shekarar 2019.
Sauran mukaman nasa sun hada da jakadan Chadi a Faransa, Spain, Portugal, Girka da kuma Vatican. Ya kuma kasance babban mai ba da shawara ga ofishin jakadancin Chadi a Saudiyya.