IQNA

Martanin Kungiyar Hamas Dangane Da Matakin Zalunci Da Burtaniya Ta Dauka A Kanta

16:07 - November 19, 2021
Lambar Labari: 3486579
Tehran (IQNA) Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Palasdinawa ta Hamas ta fitar da wata sanarwa inda ta mayar da martani kan matakin da sakataren harkokin cikin gida na Burtaniya ya dauka na sanya kungiyar cikin 'yan ta'adda.

Shafin yada labarai na Falastinu ya bayar da rahoton cewa, bayanin na Hamas ya ce; sakatariyar harkokin cikin gida ta Buritaniya, Britt Patel ta kira kungiyar Hamas a matsayin kungiyar ta'addanci tare da yi wa magoya bayanta barazanar daurin shekaru 10 a gidan yari.

Sai dai abin takaicin shi ne, Buritaniya tana ci gaba ne da maimaita wautar da ta yi a baya, maimakon ta nemi gafarar al'ummar Palastinu da kuma gyara kuskuren tarihi da ta yi wa wannan al'umma, dangane da mummunan kudirin Balfour ya dauka, da kuma mulkin mallakar Burtaniya a kan Falastinu, wanda Burtaniya ce ta mika Falastinu ga yahudawan sahyuniya domin su mayar da ita kasarsu, inda tare da taimakon Burtaniya yahudawa suka kafa Isra'iila a cikin Falastinu.
 
Bayanin ya ce wannan ya ishi Burtaniya abin kunya a tarihi har kasa ta nade, amma kuma ba ta takaitu da hakan ba, har sai ta sake dawowa tana taimaka ma Isra'ila domin murkushe al'ummar Falastinu masu gwagwarmayar neman 'yancinsu da rayuwa cikin karama da mutunci.
 
Haka nan kuma bayanin ya kara da cewa, keta alfarmar wurare masu tsarki da kuma tsorata masu ibada da tozarta su, da kwace wurare na al'ummar Falastinu da gina matsugunnan yahudawa 'yan share wuri zauna da Isra'ila ke yi da kai hare-hare a kan fararen hula da yi musu kisan gila, wannan shi ne ta'addanci na hakika.
 
 

4014489

 

captcha