Shafin Geen Faith ya bayar da rahoton cewa, Kungiyar ta Islamic Association of North America ta rattaba hannu a kan wannan tare da yin kira ga sauran addinai da su fitar da sanarwar hadin gwiwa don nuna goyon baya ga yarjejeniyar.
A cikin abubuwan da yarjejeniyar ta kunsa dai hard a daukar matakai na kiyaye gurbatar muhalli ta fuskar hana zubar da abubuwa da za su iya kawo kawo gurbatarsa.
Haka ya hada da zubar da robobin da aka gama amfani da su, ko kuma gurbataccen mai, ko fitar da hayaki na ababen hawa masu matsala da makamantan hakan.
Kungiyar ta ce daukar wannan mataki na alaka ne da ‘yan adamtaka da kuma kare rayuwar bil adama da muhallainsu na rayuwa.