Jaridar Daily Maverick ta bayar da rahoton cewa, Shugaban na Afirka ta Kudu ya yi gargadin ne a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da takwaransa na Kenya, Uhoru Kenyatta, game da barazanar kungiyar ISIS da makamantansu a Afirka ta Kudu, yana mai cewa ba za a taba yin watsi da barazanar tayar da kayar baya ba, sannan a mai da hankali kan kasa guda dunkulalliya.
Ramaphosa ya ce, Wadannan kungiyoyi da suka zo da sunaye daban-daban suna da hadin gwiwa a tsakaninsu wajen gudanar da ayyukansu na ta'addanci, Saboda haka, a matsayinmu na kasashen nahiyar Afirka, dole ne mu dauki matakan da suka dace ta hanyar hadin gwiwa tare da hada kai wajen musayar bayanai, yin aiki tare, da kuma bin diddigin wadannan 'yan ta'adda a duk inda suke.