IQNA

Kungiyoyin Gwagwarmayar Iraki Na Kan Bakansu Na Fitar Da Amurka Daga Kasarsu

18:09 - December 10, 2021
Lambar Labari: 3486666
Tehran (IQNA) Kungiyoyi masu gwagwarmaya da ‘yan ta’adda a kasar Iraki sun sha alwashin ci gaba da gwagwarmaya da sojojin Amurka a kasar har zuwa lokacin da zasu fice daga kasar.
Kungiyar Nujba ta sanar cewa, duk da cewa gwamnatin Amurka ta bada sanarwan cewa ta kawo karshen aikin abinda ta kira yaki da ta’addanci a kasar Iraki, amma mun san ita ba abar amincewaba ce, don haka kungiyar zata ci gaba da gwagwarmaya da sojojin Amurka a kasar har sai sun fice daga kasar.
 
Nasr al-Shammari, kakakin kungiyar ya shaidawa tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon kan cewa, idan sojojin Amurka basu fice daga kasar Iraki zuwa karshen wannan shekarar ba, zasu ci gaba da daukarta a matsayin sojoji mamaya, sannan zasu dub duk hanyoyin da ya sawwaka don ganin ta fice daga kasar.
 
Kafin haka Qassim al-Araji, mai bawa gwamnatin kasar Iraki shawara ya bada sanarwan cewa an kawo karshen kawancen Amurka na yakar ‘yan ta’adda a kasar Iraki.
 
 
https://iqna.ir/fa/news/4019759
captcha