IQNA

Jami'an 'Yan Sandan Amurka Sun Kama Mutumin Da Ya Kona Kur'ani A Jami'ar Arizona

23:48 - December 12, 2021
Lambar Labari: 3486676
Tehran (IQNA) An kama wani mutum da 'yan sandan suka ce shi ne ke da alhakin lalata da kona littattafan addinin Musulunci da kwafin kur'ani a jami'ar Arizona ta Amurka.

Tashar Alhurra ta bayar da rahoton cewa, ‘Yan sanda a Jami’ar Arizona sun kaddamar da bincike kan zargin lalata litattafan addinin Islama da kuma wulakanta kur’ani mai tsarki a dakin karatu na jami’ar a ranar Larabar da ta gabata, tare da cafke wani mutum da ke da hannu a lamarin.

Kafin kama shi, Majalisar musulmin Amurka ta bayyana lamarin a matsayin laifin kiyayya, sannan kuma ta ce dalibai musulmi suna zaune lafiya da kowa tsakaninsu da sauran dalibai.

Kungiyar dalibai musulmi ta Jami’ar Arizona ta kuma sanya hotunan konawa da yayyage shafukan littattafan larabci da barnar da aka yi a dakin karatu a shafukan sada zumunta.

‘Yan sanda sun kama wani mutum mai shekaru 38 a ranar Alhamis, 9 ga watan Disamba, bayan wani shaida ya gan shi yana yaga littattafai da mujallu. ‘Yan sanda sun ce mutumin ne ke da alhakin lalata littattafan addinin musulunci a jami’ar Arizona, kamar yadda faifan bidiyo na CCTV ya nuna.

 

4020291

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa:
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha