IQNA

An tabbatar da nadin musulmi na farko da zai wakilci Amurka a harkokin 'yancin addini

21:22 - December 19, 2021
Lambar Labari: 3486704
Tehran (IQNA) Majalisar dattawan Amurka ta amince da ayyana musulmi da Joe Biden ya yi a matsayin wakilin Amurka na farko kan harkokin ‘yancin addini.

Tashar TRT ta bayar da rahoton cewa, a wani mataki wanda shi ne irinsa na farko a kasar Amurka,  Majalisar Dattawan kasar ta ayyana Rashad Hussein, Ba'amurke musulmi a matsayin wakilin Amurka kan 'yancin addini.

 
Rashad Hussein, wanda shugaban Amurka Joe Biden ya gabatar da sunansa a watan Yuli, ya samu amincewar majalisar dattawan Amurka da kuri'u 85 da suka amince da shi, yayin da 5 suka ki amincewa. Hussein shi ne musulmin Amurka na farko da aka zaba a kan wannan mukami.
 
Rashad Hussein ya taba rike mukamin jakada na musamman a kungiyar hadin kan kasashen musulmi, da wakili na musamman kan yaki da ta'addanci, da mataimakin mai baiwa fadar White House shawara a gwamnatin tsohon shugaban Amurka Barack Obama.
 
Kungiyar (CAIR) babbar kungiyar kare hakkin musulmi a Amurka, ta yi maraba da nadin, da cewa: “Wannan rana ce mai cike da tarihi ga al’ummar Musulmin Amurka da kuma al’ummarmu,” a cewar Edward Ahmed Mitchell, mataimakin darektan zartarwa na majalisar a wata sanarwa.
 
Mitchell ya kara da cewa: "Muna da tabbaci kan cewa Rashad Hussein zai kare 'yancin addini na dukkanin al'ummomin da ke fuskantar barazanar kyama a duniya, ciki har da Musulman Uighur na China."
 
Hukumar 'Yancin Addini ta Amurka ta kuma yi maraba da nadin Hussein, inda ta sanar da cewa, "Rashad Hussein, tare da shekarunsa na ilimi da gogewa, yana da kyakkyawar dama wajen gudanar da abin da ya dace wajen kare hakkokin dukkanin mabiya a ddinai a duniya."
 
A watan Agustan da ya gabata, Joe Biden ya ayyana Rashad Hussein a matsayin jakadan kasar Amurka kan 'yancin addini na kasa da kasa, a baya ya taba rike mukamin Darakta na kungiyar hadin gwiwa  ta duniya a kwamitin tsaron kasa na Amurka.
 
 
captcha