IQNA

Iran Ta Ce Ba Ta Karbar Izinin Kowa Domin Inganta Ayyukanta Na Tsaro

23:02 - December 25, 2021
Lambar Labari: 3486727
Tehran (IQNA) Iran ta sanar da cewa ba ta karbar izini daga kowa a duniya domin inganta ayyukanta na tsaro.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Saeed Khatibzadeh ya ce, kasarsa ba ta karbar izini daga kowa a duniya domin inganta ayyukanta na tsaro.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran yayin da yake yin watsi da matsayin ma'aikatar harkokin wajen kasar Burtaniya na shiga tsakani kan karfin tsaron kasarsa ya ce: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana aiki ne bisa tsarin dokokin kasa da kasa, daidai da bukatun tsaronta, inda ya ce furucin na Burtaniya shiga cikin harkokin cikin gida ne na Iran, tare da yin harshen damo a kan batutuwa na siyasa da suka shafi Iran da kuma wasu kasashen yankin.

Ya ce a yayin da ake gasar sayar da makamai masu matukar hadari a yankin gabas ta tsakiya da ma duniya, wanda hakan yake kara ruruta wutar rikicia  yankin, Burtaniya tana daga cikin masu sayar da wadannan muggan makamai, amma kuma a lokaci guda ita ce ke magana kan rashin halascin makaman Iran, ko kuma take ikirarin cewa barazana ne ga wasu kasashe daga cikin kasashen da take sayarwa da muggan makamai.
 
 
 
 
 

 

 

4023215

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kowa ، a duniya ، inganta ، kasar Iran ، Inganta Ayyukant
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha