IQNA

An Kai Hari A wani Masallaci A kasar Jamuss

22:41 - January 24, 2022
Lambar Labari: 3486863
Tehran (IQNA) An harbe wani masallaci a jihar Saxony-Anhalt da ke gabashin Jamus. yan sanda na ci gaba da bincike kan wannan lamari.

'Yan sandan Jamus sun ce an kai hari kan wani masallaci a jihar Saxony-Anhalt da ke kasar.

A cewar jami’an ‘yan sanda, mutane biyu ne suka ji karar harbe-harbe a kusa da cibiyar al’adun Musulunci dake hade da masallaci ta Haleh inda suka sanar da ‘yan sanda. kuma 'Yan sanda sun gano harsashi uku a wurin.

Shaidun gani da ido sun lura cewa wani mutum dan shekara 55 ne ya yi harbi shi daga gidansa da ke kusa da  masallacin.

Wannan dai ba shi ne karon farko da masu akidar tsananin kiyayya da muuslmi suke kai hari kan masallatai da cibiyoyon addinin musluncia  kasar Jamus ba.

Masu akidar kin jinin musulmi a Jamus da wasu daga cikin kasashen turai suna kallon musulmi a matsayin barazana ga makomar kasashensu, musammn musamamn yadda adadin musulmi yake bunkasa a cikin kasashen turai.

captcha