IQNA

An binne gawar Ayatullah Lutfollah Safi a kusa da kabarin Imam Hussain (AS)

22:18 - February 03, 2022
Lambar Labari: 3486901
Tehran (IQNA) A yammacin yau ne aka yi janazar babban malami Ayatollah Safi a hubbaren Imam Hussain (AS) inda aka binne gawarsa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a yammacin yau ne aka yi janazar bababn malami Ayatollah Safi a hubbaren Imam Hussain (AS) inda aka binne gawarsa.

Dubban mutane ne suka halarci janazar tasa inda aka kai munkarar da ke dauke da shi a hubbaren Imam Husaini (AS) da Sayyid Abbas (AS) a Karbala a yammacin yau.

An gudanar da jana'izar wannan malami mai tsoron Allah a tsakanin haramomi biyu na Karbala masu alfamrma, tare da halartar malamai da muminai tare da yi masa addu'a.

Ayatullahi Safi Golpayegani a ranar Litinin din wannan makon bayan jinya da ya yi, ya rasu yana da shekaru 103 a birnin Qum na kasar Iran.

https://iqna.ir/fa/news/4033603

captcha