IQNA

Sarkin Qatar Ya Isar Da Sakon Taya Murnar Zagayowar Ranar Juyin Musulunci A Iran

19:49 - February 11, 2022
Lambar Labari: 3486938
Tehran (IQNA) Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani ya aike da sakon taya murna ga shugaban kasar Iran kan zagayowar ranar samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar.

Kamfanin dillancin labaran kasar Qatar ya habarta cewa, sarkin kasar Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani ya aike da sako ga shugaban jamhuriyar musulunci ta Iran Seyyed Ibrahim Raisi tare da taya shi murnar zagayowar ranar kasa ta Iran.

A gefe guda kuma ofishin jakadancin kasar Iran a kasar Qatar ya sanar da gudanar da taron tunawa da zagayowar ranar samun nasarar juyin juya halin musulunci a kasar Iran, tare da halartar jami'an kasar Qatar da wasu gungun 'yan kasar Iran mazauna kasar ta Qatar, da kuma jami'an diflomasiyya na wasu kasashen duniya.

 

4035569

 

 

captcha