IQNA

Tarukan Ibada Na Etikaf A Masallatan Tanzania

23:39 - February 17, 2022
Lambar Labari: 3486951
Tehran (IQNA) Daraktan Sadarwa na Wakilin Jami’ar Mustafa (AS) a Tanzaniya ya sanar da gudanar da horo na Etekaf Rajabiyya a karon farko a tarihin Tanzaniya wanda Wakilin jami’ar Mustafa (AS) ya gudanar a Dar es Salaam.

Ahmad Ramezani, malami mai wakilcin jami'ar Al-Mustafa ta kasa da kasa da ke Tanzaniya a yau 17 ga watan Fabrairu a wata hira da ya yi da IQNA, yayin da yake taya murnar zagayowar ranar haihuwar Amirul Muminin Imam Ali (AS) ya sanar da cewa: A kasar Tanzania an gudanar da shi a manyan masallatai guda biyu a birnin Dar es Salaam.

ارسالی/مراسم معنوی«اعتکاف رجبیه» برگزار شد

Malamin jami'ar Al-Mustafa Al-alamiyah ya kara da cewa: I'itikafi daya ne daga cikin muhimman ibadu na Musulunci da suka yadu sosai musamman bayan juyin juya halin Musulunci, kuma ya haifar da wani sabon yanayi na ruhi.

I’itikafi wani nau’i ne na kau da kai daga yanayin rayuwa na yau da kullum domin mutum ya samu kusanci ga Allah.

Ya ce adadin wadanda suka halarci wannan horo ya kai 210 malamai maza da mata.

ارسالی/مراسم معنوی«اعتکاف رجبیه» برگزار شد

 

https://iqna.ir/fa/news/4036887

 

 

captcha