IQNA

Gwamnatin Sahayoniya ce ta haifar da tabarbarewar alakar Aljeriya da Maroko

23:45 - February 17, 2022
Lambar Labari: 3486952
Tehran (IQNA) Shugaban kasar Aljeriya Abdel Majid Taboun ya bayyana alakar kasarsa da Maroko a matsayin mai duhu, ya kuma zargi gwamnatin sahyoniyawan da tada zaune tsaye.

A wata hira da ya yi da kafafen yada labaran kasar, Tebon ya ce Maroko na amfani da "farfaganda da labaran karya" a kowace rana wajen kai hari kan hadin kan kasa da cin mutuncin sojojin kasar Aljeriya.

Ya yi nuni da cewa gwamnatin sahyoniya tana goyon bayan Maroko a kan Aljeriya.

Tebon ya tabo batun ne a matsayin martani ga tambayar ko har yanzu shugaban na Aljeriya yana kan matsayin da ya bayyana a wata ganawa makamancin haka da ya yi da kafafen yada labaran Aljeriya a watan Oktoban da ya gabata.

Tebon ya bayyana a wannan taron cewa: kasarsa ba za ta amince da duk wani shiga tsakani da kasar Maroko domin maido da alakar da ke tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata ba. A wancan lokacin dai kasar Aljeriya ta bayyana wannan sanarwa a matsayin wani mataki mai tsauri, wasu kuma suka kira ta gargadi ga gwamnatin sahyoniyawan kan illar da ke tattare da kai hari a kasar Aljeriya.

 

https://iqna.ir/fa/news/4036922

 

captcha