IQNA

Jawabin Sayyid Nasrullah Dangane Da Ranar Shahidan Gwagwarmayar Hizbullah

23:48 - February 17, 2022
Lambar Labari: 3486953
Tehran (IQNA) Babban sakataren kungiyar Hizbullah ya bayyana cewa Emad Mughniyeh wata alama ce ta ci gaban tsayin daka domin kare kasar Labanon.

Sayyid Hassan Nasrullah babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya bayyana cewa shahidi Haj Emad Mughniyeh wata alama ce ta ci gaban tsayin daka domin kare kasar Labanon, ta ci gaba da taimakawa al'ummar Palastinu, da kare birnin Kudus.

A yau ne babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah ya gabatar da jawabi a wajen bikin karrama shuwagabanni kuma shahidan gwagwarmaya da kungiyar Hizbullah ta shirya a zauren majalisar Sayyid al-Shuhada da ke yankunan kudancin birnin Beirut.

A farkon jawabinsa bayan yabon Allah da manzonsa zababbun ya taya murnar zagayowar ranar haihuwar Amirul Muminin Ali Ibn Abi Talib (AS) inda ya ce: Idan muka ambaci sunan Ali (as) muna godewa Allah Maɗaukakin Sarki kan tarbiyar da iyayenmu da suka ba mu, sun rene mu tun ƙuruciya bisa sonsa wanda shi ne son manzon Allah da Alayensa masu tsarki.

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, yayin da yake ishara da shahidan gwagwarmayar gwagwarmaya ya bayyana cewa: Shekaru 38 da shahadar Sheikh Ragheb Harb, shekaru 30 da shahadar Sayyid Abbas al-Musawi tare da Mujahid Umm Yasir da dansu Hussein, sannan kuma ya ce: Shekaru 14 da shahadar Haj Emad Mughniyeh, shugaba Jihadi wanda ya cika shekaru 40 da fara aikin gwagwarmayar Musulunci da Hizbullah.

Ya kira shekarar 1982 shekarar da aka saka dan ba na farkon aiki da kuma ci gaban wanzuwar gwagwarmayar Hizbullah, ya ce: Jinin shahidanmu ya tabbatar da wannan tafarki.

 

https://iqna.ir/fa/news/4036900

 

captcha