IQNA

Wani Malamin Kur’ani A Masar Ya Horar Da Dubban Mahardata Kur’ani

0:03 - February 18, 2022
Lambar Labari: 3486954
Tehran (IQNA) Eid Amer wani shehi dan kasar Masar ne wanda ya koyar da dubban yara hardar kur’ani kyauta ga a kauyensu tsawon shekaru 30 da suka gabata.

Eid Amer, babban malamin haddar Alkur’ani mai girma ne, wanda a yanzu haka ya tsufa ya fara kamashi shi, yana mai cewa ,  Shekaru 30 da suka gabata na yi nasarar ziyartar Makka da dakin Allah tare da samun albarka da ke wannan harami mai tsarki., a lokacin Tawafi na isa Dutsen Hajrul Aswad sai na yi addu’a Allah Ya sa na kasance cikin masu haddar Alqur’ani mai girma.

Wani mazaunin kauyen Mit Abu Qom da ke birnin Tala a lardin Al-Manoufiyah na kasar Masar ya ce, ya samu nasarar haddar kur’ani mai tsarki cikin kankanin lokaci kuma yana da niyyar koyar da yaran kauyen Al-kur’ani; Musamman bayan rasuwar Sheikh Abdul Hamid malamin haddar kur'ani a kauyen, babu wanda ya kafa Darul-Qur'ani na yara.

Ya kara da cewa: “Da farko mutanen kauyen ba su yi tunanin cewa wani yana da shirin koyar da haddar Alkur’ani ga yaran kauyen ba; Amma a lokacin da na fara aiki da yara da matasa da dama, mutanen kauyen sun fi sanina, har ma suna kawo ’ya’yansu daga kauyukan da ke makwabtaka  don haddace Alkur’ani.

Sheikh Amer ya ce, yana bayar da lokacinsa ne tun daga safe zuwa la'asar wajen koyar da kur'ani kyauta.

 

https://iqna.ir/fa/news/4037044

 

captcha