IQNA

Hukumomin Saudiyya sun sako malamin Iraqi

16:53 - March 04, 2022
Lambar Labari: 3487012
Tehran (IQNA) Shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Ahd News ya habarta cewa, an saki Sheikh Walid al-Zaidi, wanda jami’an Saudiyya suka tsare a kwanakin baya a lokacin da yake gudanar da aikin Umrah a birnin Makkah.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iraki Ahmed al-Sahaf ya shaida wa tashar talabijin ta Al-Ahd jiya da yamma cewa "ana ci gaba da bin diddigin lamarin Sheikh Walid al-Zaidi da kuma yadda aka samu labarin tsare shi a cikin Saudiyya."
Sai dai bai yi karin bayani kan yunkurin korar malamin na Shi'a ba.
Jami’an Saudiyya sun kama Sheikh Waleed al-Zaidi, wanda ya tafi kasar Saudiyya a kwanakin baya a wani ayari mai alaka da hukumar Hajji da Alhazai ta kasar Iraki, a lokacin da yake gudanar da aikin Umrah a Makka shi da matarsa ​​da ‘ya’yansa.
Riyadh bai bayyanawa iyalan Al-Zaidi dalilin da yasa aka tsare shi ba.
Hukumar Hajji da Alhazai ta Iraki ta kuma aike da sako ga mahukuntan Saudiyya a ranar Larabar da ta gabata, inda ta bukaci a sako 'yan Irakin da ake tsare da su da suke gudanar da aikin Umrah a kasar.
 
https://iqna.ir/fa/news/4040045

Abubuwan Da Ya Shafa: Sheikh Walid al-Zaidi,
captcha