IQNA

Ziyarar Babban Hafsan Sojojin Isra'ila a Bahrain

18:52 - March 10, 2022
Lambar Labari: 3487033
Tehran (IQNA) A jiya ne Aviv Kukhawi ya isa Bahrain a karon farko a wata ziyarar bazata inda ya gana da jami'an Bahrain da kuma kwamandan rundunar sojin Amurka ta biyar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Aljazeera cewa: Janar Ziab bin Saqr al-Nuaimi babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Bahrain ya tarbi Kukhawi bayan ya isa filin tashi da saukar jiragen sama.

Rundunar sojin Isra'ila ta fitar da sanarwa inda ta bayyana ziyarar da babban hafsan hafsoshin sojin Isra'ila ya kai Bahrain a matsayin mai tarihi.

Kukhawi ya gana da takwaransa na Bahrain, Nasser bin Hamad Al Khalifa, mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasa kuma babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Bahrain.

Sanarwar ta ce, baya ga kwamandan rundunar sojin Amurka ta biyar, Kokhawi ya shirya ganawa da wasu jami'an soji da shugabannin Bahrain a hedikwatar rundunar da ke Bahrain.

Ziyarar da ba a bayyana ba ta kuma hada da wasu jami'an sojin Isra'ila da suka hada da shugaban nazarin leken asiri na soji da kuma shugaban tsare-tsare da komiti na uku, jami'in soji mai kula da harkokin Iran.

Wasu masana dai na alakanta ziyarar Kukhawi a Bahrain da yanayin tattaunawar nukiliyar Iran a Vienna.

Masu fafutuka na zamantakewa da siyasa da na Bahrain sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da ziyarar jami'an gwamnatin yahudawan sahyoniya,

https://iqna.ir/fa/news/4041879

captcha