
Kamfanin dillancin labaran Anatoly ya bayar da rahoton cewa, Abdul Rahman Al-Sudais babban daraktan kula da harkokin harami na kasar Saudiyya ya sanar da cewa za a ci gaba da gudanar da tarukan I’itikafi a masallacin Harami da na Masallacin Nabi (A.S) bisa wasu tsare-tsare da ka’idoji na musamman.
Abdul Rahman Al-Sudais ya kara da cewa a cikin wata sanarwa da ya fitar: Za a gudanar da i'itikafi ne a goman karshe na watan Ramadan, kamar yadda Manzon Allah (S.A.W) ya yi a wurare guda biyu masu alfarma.
Ya sanar da hakan ba tare da wani karin bayani ba yana mai cewa: “Ba da jimawa ba za a samu bayanin dawowar I’itikafi a Masallacin Harami da Masallacin Nabi ta shafin yanar gizo na haramin guda biyu, bisa la’akari da wasu sharudda da suka dace, da kuma samun lasisi."
Sakamakon bullar cutar Corona, jami’an Saudiyya a shekarar 2020 da 2021 sun yanke shawarar hana i’itikafi a masallatai a cikin watan Ramadan a wani mataki na hana yaduwar cutar corona a kasar.
A ranar 6 ga Maris, Saudiyya ta ba da sanarwar dakatar da daukar matakai da ka'idoji masu tsauri na hana yaduwar cutar.
https://iqna.ir/fa/news/4044673