IQNA

Wakilan addinai da ƙungiyoyi sun hallara a Malawi

23:05 - March 27, 2022
Lambar Labari: 3487098
Tehran (IQNA) Wakilan addinai da mazhabobi sun taru a cibiyar Musulunci ta Malawi domin karawa juna sani kan mai ceton duniyar dan Adam da kuma Imam Mahdi (a.s).

A yayin wannan taron wasu baƙi sun gabatar da jawabai tare da bayyana ra'ayoyinsu game da mai ceto na karshen zamani.

"Ba ni da masaniya game da Mai Ceto da Wanda aka yi Alkawari ta wannan hanya, dole ne in kara zuwa wannan cibiyar in koya daga gare ta," in ji Rev. Jovau. A da ina tsoron musulmi, amma yanzu na ga cewa Musulunci shi ne mafi alheri.

Sheikh Mulova daya daga cikin shehunan Ahlus-Sunnah a yankin ya ce : Manzon Allah SAW ya kwadaitar da mutunta makwabci ba tare da la’akari da addininsa ba ko kabilarsa.

"Sheikh Abu Bakr Wendelra" na Ahlus Sunnati Kadiriyah na Malawi ya kara da cewa: "Na yi matukar farin ciki a yau cewa mazhabar Ahlul Baiti (AS) ne kadai ke da ikon hada kan al'ummar duniya ba tare da la'akari da addininsu ba."

“A kowane hali, mu musulmi ne ko kirista, amma mu sani cewa Allah ne zai hukunta mu saboda ayyukan da muka aikata (mai kyau ko mara kyau),” in ji Fasto Emmanuel Jafar. Mu duka mutane ne kuma ya kamata mu rayu tare da abota da ƙauna ga juna.

"Ya zama dole a ko da yaushe a yi magana game da mai ceto," in ji Rev. Patrick Sami na Cocin Pentikostal a Shalom. Don haka dukkanmu (Musulmi da Kirista) muna cikin wani yanayi na duniya, don haka muna bukatar wanda ba shi da wata matsala ya cece mu, domin mutanen da ke cikin rikici ba za su iya ceton juna ba.

نمایندگان ادیان و مذاهب در مالاوی گردهم آمدند

https://iqna.ir/fa/news/4045137

captcha