IQNA

An Shimfida Sabbin Dardumomi Guda 25,000 A Masallaci Haramin Makka Mai Alfarma

15:29 - April 03, 2022
Lambar Labari: 3487118
An Shimfida Sabbin Dardumomi Guda 25,000 A Masallaci Haramin Makka Mai Alfarma
Tehran (IQNA) Hukumomin kasar Saudiyya sun sanar da cewa an shimfida sabbin kafet guda 25,000 a masallacin harami yayin da aka fara azumin watan Ramadan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar  Russia Today cewa, babban daraktan kula da masallacin mai alfarma da kuma masallacin manzon Allah s.a.w ya sanar da cewa, an samar da sabbin dardumomi guda 25,000 a masallacin mai alfarma domin tarbar masu ibada a cikin watan azumin Ramadan.

Jaber Ahmad Wadani, shugaban sashen tsaftace dardumomi  na masallacin Harami, ya ce: “Sabbin kafet din sun kasance nau’in koren kafet na alfarma na kasar Saudiyya, domin masu ibada su rika gudanar da ibadarsu cikin kwanciyar hankali da girmamawa.

Wadani ya jaddada cewa: Ana gudanar da wadannan ayyuka bisa kokarin Abdul Rahman bin Abdul Aziz Al-Sadis babban daraktan masallacin Harami da Masallacin Annabi, da nufin tabbatar da muradun mahukunta a kasar Saudiyya, don samar da mafi kyawun ayyuka hidima a wuraren ibada guda biyu masu tsarki ”.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4046216

captcha