
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga Farance 24 cewa, Khalid al-Darby daya daga cikin mashahuran masu gyaran kur'ani mai tsarki a kasar Libiya na daya daga cikin masu wannan aiki da ke zuwa wani taron bita a birnin Tripoli a kullum domin biyan bukatu masu yawa na kwastomomi a cikin watan Ramadan.
Al-Darby ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, ana samun karuwar sayen sabbin kur'ani a bisa al'ada kafin watan Ramadan, amma a baya-bayan nan lamarin ya sauya a Libiya.
Ya kara da cewa: Sayen wannan littafi mai tsarki ya yi matukar wahala musamman ganin yadda gwamnati ta daina buga kur'ani a kasar Libiya.
Kasar da ke arewacin Afirka ta shafe fiye da shekaru goma tana fama da tashe-tashen hankula, kuma da yawa daga cikin cibiyoyinta sun durkushe, lamarin da ya yi mummunar illa ga kasar mai arzikin man fetur.

Al-Darby yana cewa: "Kudin sayen kur'ani ya karu, don haka gyaran tsoffin kur'ani ya zama wanda ba a taba ganin irinsa ba a kasar."
Idan aka kwatanta da farashin sabon kur’ani, wanda ya haura dalar Amurka 20, Al-Derby ya ce daloli kadan ne kawai zaa bayar don gyaran kur’ani. Amma kuma batun tsada ba ne kawai a cikin al'amarin, mutane da yawa suna kallon tsoffin kur’anai a matsayi na musamman.