Tehran (IQNA) Da safiyar yau Asabar ne dai sojojin Isra'ila su ka sanar da shelanta kai hari a kusa da garin Jenin da kuma a cikin sansanonin Palasdinawa ‘ yan gudun hijira da kuma garin Barqin.

Fara kai farmakin na yau ya zo ne bayan da ‘ yan sahayoniyar su ka girke rundunoni uku na soja a yammacin kogin Jordan.
Ma’aikatar kiwon lafiya ta Palasdinwa ta sanar da cewa; Bapalasdine daya mai suna Ahmad al-Sa’adi ya yi shahada sanadiyyar harbinsa da ‘ yan sahayoniyar su ka yi a kansa da kuma kirjinsa.
Bugu da kari wasu Palasdinawa da dama sun jikkata sanadiyyar farmakin na sojoin sahayoniya a yankin na yammacin kogin Jordan.
Da safiyar yau Asabar din an yi musayar wuta a tsakanin sojojin Sahayoniyar da kuma Palasdinawa a cikin sansanin ‘yan gudun hijrar na Jenin.