Tehran (IQNA) A daidai lokacin da aka shiga rana ta takwas ga watan Ramadana, an buga karatun kur'ani mai tsarki juzu'i na takwas da muryar Qasem Razi'i, makarancin kasa da kasa na kasarmu, wanda aka buga a kafar yada labarai ta IQNA.

Karatun kur'ani mai tsarki gaba daya a cikin watan ramadana ta zama wata dama ga mutane da yawa wajen sanin kur'ani mai tsarki a cikin wadannan shekaru.
Dangane da haka ne IQNA za ta rika sanya wani bangare na kur'ani mai tsarki a kowace rana a cikin watan Ramadan na shekara ta 2022 da muryar Malam Qasim Radi'i, malami kuma mai karatun kur'ani mai girma na duniya.
