Akwai hadisai da dama a cikin littafan ruwaya game da ibadojin azumi.
Yanzu kuma a cikin watan Ramadan mai alfarma, za mu yi bayanin wasu daga cikin ibadojin azumi da aka ambata a cikin littafin nan mai suna "Kunz al-Maram fi Amal Shahr al-Siyam" :
1. Kare sassan jiki daga aikin da bai dace ba. Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Duk lokacin da aka wa mai azumi zancen da bai dace ba, sai ya ce: Assalamu alaikum, ina azumi, Allah ya ce: Bawana ya fake da azumi, ku tsare shi daga wuta, ku shigar da shi Aljanna." Imam Baqir (AS) ya kuma ce: “Duk wanda ya azumci kwanakin watan Ramadan, kuma ya raya wani bangare na dararensa yana ibada, ya kame cikinsa da sha’awarsa, ya tsare idanunsa da harshensa, ya hana fitina tsakanin mutane, ya kuma nisanci zunubai.” Ya zama mai tsarki kamar ranar da aka haife shi.
2. Ka guji dandana, ci da sha
3. Kamshin turare da wardi da makamantansu. Kamar yadda Imam Sadeq (AS) yake cewa: " Turare kyauta ce ga mai azumi ".
4. Ka guji wurare marasa kyau da na nishaɗi
5. Tsabtace zuciya daga abubuwa kamar girman kai, hassada da ....
6. Yin azumi a boye, don gujewa girman kai da munafunci
7. Yin zikiri a cikin watan Ramadan
8. Kar a sanya tufafi na alfarma da kasaita
9. A guji zama a cikin ruwa (don kula kada ruwa ya shiga jiki).
10. A guji ba'a ko da tsakanin ma'aurata ne
12. Ka guje wa tafiye-tafiye, ban da aikin hajji da tafiye-tafiye masu mahimmanci
2. A guji tauna wani abu a baki