IQNA

Karatun Abdul Basit a Masallacin Sheikh Zayed dake Abu Dhabi

16:44 - April 17, 2022
Lambar Labari: 3487180
Tehran (IQNA) Ustaz Abdul Basit Mohammed Abdul Samad, shahararren makaranci dan kasar Masar ne a lokacin rayuwarsa, ya zagaya kasashe da dama ciki har da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, inda ya yi karatun kur'ani mai tsarki, ya kuma bar abubuwan tunawa a wadannan kasashe.

A rahoton iqna, Masallacin Sheikh Zayed bin Sultan Masallacin da ke Abu Dhabi UAE,  Wannan masallaci  shi ne masallaci na uku mafi girma a duniya bayan Masallacin Harami da kuma Masallacin Annabi, kuma yana daya daga cikin abubuwan da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ke alfahari da su.

Masallacin yana cikin wani katafaren wuri tsakanin gadoji biyu a kofar Abu Dhabi.

Za ku ji nassin karatun suratu Hood daga bakin Ustaz Abd al-Basit Abd al-Samad a cikin wannan masallacin albarkacin watan Ramadan a shekarar 1980:

 

https://iqna.ir/fa/news/4049844

 

captcha