IQNA

Falastinawa 'Yan Gwagwarmaya Sun Mayar Wa Isra'ila Da Martani Da Rokoki Daga Gaza

18:00 - April 23, 2022
Lambar Labari: 3487204
Tehran (IQNA) Falastinawa ‘yan gwagwarmaya a yankin zirin Gaza sun mayar da martani da makaman roka a matsugunnan yahudawan ‘yan share wuri zauna

Tashar Falasdinu Al-Youm ta bayar da rahoton cewa, bayan harin da Falastinawa ‘yan gwagwarmaya suka kai a daren jiya da makaman roka, an ji karar sautin kararrawa a matsugunan yahudawan sahyoniya da ke kusa da Gaza.

Ita ma tashar Al-Mayadin, ya nakalto daga kafafen yada labaran Isra'ila cewa, an harba makamai masu linzami guda biyu daga Gaza zuwa cikin yankunan Falastinawa da Isra’ila take mamaye da su.

Kazalika, gidajen rediyo da talabijin na sahyoniyawan sun tabbatar a cikin rahotanninsu kan cewa, an harba rokoki guda biyu daga zirin Gaza, daya daga cikinsu ya fado a wani yanki da ke kusa da zirin Gaza a wani matsugunnin yahudawa.

Dakarun gwagwarmayar Palasdinawa sun harba rokoki da dama daga Gaza zuwa matsugunan yahudawan sahyoniya da ke kan iyaka a daren Laraba da kuma safiyar Alhamis Alhamis da ta gabata, biyo bayan hare-haren da jiragen yakin Isra’ila suka kaddamar a yankin na Gaza.

 

4051713

 

 

captcha