IQNA

Fahimtar Alkur'ani ta isa ta hada kan Musulmi

19:55 - April 25, 2022
Lambar Labari: 3487215
Tehran (IQNA) Andres Richardson, farfesa a fannin ilimin tauhidi daga kasar Canada, ya jaddada cewa kur'ani mai tsarki ne a matsayin wani abu na hadin kai a wani jawabi da ya yi a daya daga cikin wuraren baje kolin kur'ani mai tsarki na kasa da kasa.

Taron mai taken "kur'ani mai tsarki a cikin batutuwan daidaiku da zamantakewa da kuma na kasa da kasa" na daya daga cikin jerin tarurruka na musamman na kasa da kasa da ke gudana a wajen baje kolin.

A farkon jawabin nasa, Richardson ya yi ishara da fahintar kur’ani mai tsarki tare da jaddada cewa daya daga cikin alamomin hakan shi ne cewa wannan littafi na Ubangiji yana magana ne a kan al’amuran da suka gabata da kuma abin da zai faru nan gaba.

Ya kara da cewa: Alkur'ani ya yi magana a kan halittu da kuma kasa da kuma lahira, kuma wannan kadai  ana iya daukarsa a matsayin shaida kan cikarsa.

Malamin tauhidin ya ci gaba da jawabinsa da jaddada cewa: Abin da Alkur'ani mai girma ya fi mayar da hankali a kai shi ne kai mutum ga Ubangijinsa.

Yayin da yake karanta tsokaci da kur'ani mai tsarki ya yi a kan batun hadin kai, ya ce: "Wannan yana daga cikin batutuwan farko da aka ambata a cikin wannan littafi na Ubangiji." Alkur'ani yana da abubuwa masu ilmantarwa wadanda kowa zai iya fahimtarsu, doomin kuwa yana Magana ne da hankali da kuma zuciya kai tsaye, saboda haka maganar kur’ani ta hada ‘yan adam baki daya.

 

4051918

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: littafi na Ubangiji
captcha