Za a gudanar da wannan biki ne a yau Alhamis 13 ga watan Oktoba a dakin taro na cibiyar Musulunci ta Imam Ali (AS), kuma ma'abota addini da masoya Ahlul Baiti (AS) za su halarta.
Cibiyar Musulunci ta Imam Ali (AS) ta kasar Sweden ta sanar a cikin sanarwar cewa: Za a fara wannan shiri ne da yamma, sannan za a gudanar da sallar Magriba da Isha'i kafin bikin da karfe 18:13 a sashin masallacin cibiyar.
Bikin ya kunshi karatun ayoyin kur’ani mai tsarki, Ibthal na yabon Manzon Allah (SAW), jawabin Hujjat-ul-Islam Abbas Bahmanpour, karatun haihuwa da gasar al’adu.
A yayin taya murnar zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah (SAW) da Imam Sadik (AS), wannan cibiya ta gayyaci 'yan uwa musulmi da masu sha'awar shiga cikin shirin.