IQNA

Hukuncin karshe na kotun Turai game da hijabi

18:09 - October 14, 2022
Lambar Labari: 3488007
Tehran (IQNA) Bayan kwashe shekaru ana cece-kuce, kotun Turai ta ayyana dokar hana hijabi a wuraren aiki.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Aljazeera cewa, bayan shafe tsawon shekaru ana takaddama a wasu kasashen turai, a yau Alhamis kotun shari’a ta turai ta fitar da wani kuduri kan yadda mata suke amfani da hijabi a wuraren aiki.

Wannan kotu ta fayyace cewa: Kamfanoni na iya haramta amfani da hijabi a wurin aiki, matukar dai wannan haramcin ya kasance na jama'a.

Wannan lamari dai yana da alaka ne da labarin wata Musulma da aka gaya mata cewa ba za ta iya sanya hijabi ba a lokacin da take shirin halartar wani horo a wani kamfani na kasar Belgium.

Dalilin wannan haramcin shi ne kasancewar wata ka’ida ta gama gari a kamfanin da ta hana a yi wa mata sutura a hedkwatarsa.

Matar dai ta mika kokenta ga wata kotun kasar Belgium, wadda ita ma ta nemi shawara daga kotun shari'a ta Tarayyar Turai.

Dangane da wannan bukata, Kotun Turai da ke Luxembourg ta fayyace cewa: Babu wariya kai tsaye a cikin wannan haramcin.

Kotun ta yanke hukuncin a shekarar da ta gabata cewa kamfanonin EU za su iya hana ma'aikata sanya hijabi a wasu sharudda idan har za su gabatar da hoton da bai dace ba ga kwastomomi.

A Jamus, dokar hana sanya hijabi ga mata a wuraren aiki ya kasance yana ta cece-kuce tsawon shekaru. Kasar Faransa wacce ke da mafi yawan musulmi tsiraru a Turai, ta haramta amfani da lullubi a makarantun gwamnati a shekara ta 2004.

4091687

 

Abubuwan Da Ya Shafa: haramta amfani lullubi kwastomomi hijabi
captcha