IQNA

An ceto Musulman Rohingya bayan wata guda suna yawo a cikin teku

15:41 - December 27, 2022
Lambar Labari: 3488405
Tehran (IQNA) An ceto wasu Musulman Rohingya da dama bayan kwashe wata guda suna yawo a cikin wani tsohon jirgin ruwa a kan teku.
An ceto Musulman Rohingya bayan wata guda suna yawo a cikin teku

Hukumomin Indonesiya sun ce sun gano dimbin 'yan gudun hijirar Rohingya a wani yanki da ke gabar teku a lardin arewacin Aceh, wadanda suka samu rauni sosai bayan shafe makonni a cikin teku suna kokarin tserewa daga mulkin sojin Myanmar.

Wannan rukuni na bakin haure 58 sun tashi ne da wani jirgin ruwa na katako, kuma a cewar wani likita dan kasar Indonesiya, uku daga cikinsu na cikin rashin lafiya sakamakon rashin ruwa.

A yayin da daya daga cikin wadannan bakin hauren ya bayyana cewa, sun shafe fiye da wata guda suna cikin teku kuma suna kokarin isa kasar Malaysia ne domin neman ingantacciyar rayuwa da rayuwa.

Kasar Myanmar mai mabiya addinin Buddah ta ware musulmin Rohingya da ke yammacin jihar Rakhine a matsayin bakin haure ba bisa ka’ida ba, kuma kungiyar ta dade tana fuskantar wariya da hana musu zama dan kasa, tafiye-tafiye, kula da lafiya da kuma ilimi.

Ana zargin Myanmar da aikata kisan kiyashi a Kotun Duniya ta Majalisar Dinkin Duniya.

Kasar da ke kudu maso gabashin Asiya ta fada cikin tashin hankali tun bayan hambarar da gwamnatin Aung San Suu Kyi a wani juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Fabrairun 2021 wanda ya kawo karshen mulkin farar hula na dan gajeren lokaci.

 

4109965

 

captcha