IQNA

An Bude Sabon Babban masallaci A kasar Ghana

18:56 - January 08, 2023
Lambar Labari: 3488468
Tehran (IQNA) An bude wani sabon masallaci a kasar Ghana tare da kokarin masu hannu da shuni da al'ummar musulmin birnin Adenta na kasar.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Modern Ghana cewa, an gina wani sabon masallaci mai suna “Masallacin Hajiya Safiya Yakubu” daga iyalan Alhaji Yakubu Kotukoli, daya daga cikin masu taimakawa birnin da kuma al’ummar musulmin Adenta.

Muhammad Marzouq Abubakar Azindu, mataimakin Usmanu Noho Sharobutu; A wajen bukin bude wannan masallaci, shugaban musulman kasar Ghana, yayin da yake jaddada muhimmancin kasancewar masallacin a cikin al'ummar musulmi, ya bukace su da su yi ibada cikin aminci da 'yan uwantaka tare da tabbatar da cewa sun gudanar da ayyukansu domin amfanin al'umma. .

Azindo ya ce: Abin da na ba da muhimmanci shi ne hadin kai, domin abin da muke gani a nan shi ne batun hadin kai. Wannan ita ce kalmar da ta hada mu duka. Musulunci ya yi umarni da a hada kanmu a kowane hali. Ina son kowa a nan ya mutunta haɗin kai yayin da bambancin.

Yakubu Mohammad Sani wanda shi ne ya kafa wannan masallacin ya bayyana cewa ta hanyar gina wannan sabon masallacin yana fatan matasan musulmin Adenta da kewaye za su zage damtse wajen neman kusanci da Allah da kuma daukar ibada da muhimmanci.

Yakubu Mohammed Sani wanda shi ne daraktan kungiyar Action Aid a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, ya bayyana a wurin taron cewa, yana gina karin masallatai biyu a yankin arewacin Ghana.

Gina masallaci da taimakon masallatai na daya daga cikin hanyoyin da masu hannu da shuni a kasar nan suke yi na taimakon al'ummar gari.

 

4112696

 

captcha