Tehran (IQNA) Iyalan wani yaro da ya nutse a ruwa a kasar Jordan a baya-bayan nan sun sanar da cewa yana daya daga cikin mahardatan kur’ani mai tsarki.

A cewar kafar yada labarai ta Press B, Amer Abu Al-Hijah yaro ne dan shekara 5 dan kasar Jordan wanda ya nutse kuma ya mutu a ambaliyar da ta afku a garin Zarqa na baya-bayan nan.
A cewar kawun wannan karamin yaro yana daya daga cikin mahardatan kur’ani mai tsarki kuma ya samu nasarar haddace sassa uku na kur’ani kafin rasuwarsa.