Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Khaleej Times cewa, dan sama jannatin kasar Emirate Sultan Al Niyadi zai shafe watanni shida masu zuwa a tashar sararin samaniya ta kasa da kasa; Wannan yana nufin zai yi azumin Ramadan da Idin Al-Fitr a sararin samaniya.
Wannan ya haifar da tambayoyi game da yadda ake azumi da addu'a a sararin samaniya. Ta yaya za ku yi azumi a sararin samaniya yayin da tashar sararin samaniya ta duniya ke zagayawa duniya sau 16 a cikin sa'o'i 24 kuma 'yan sama jannatin da ke cikinta sun shaida fitowar rana 16 da faɗuwar rana 16 a rana ɗaya ta duniya?
Ismail Mufti Manek wani malami mai wa’azi daga kasar Zimbabwe wanda shahararren malami ne, ya ce ba wajibi ne a yi azumi ba saboda dan sama jannatin yana tafiya.
Ya ci gaba da bayanin ka’idoji da tsawon lokacin azumi a tashar sararin samaniyar kasa da kasa idan dan sama jannatin ya bukaci yin azumin watan Ramadan mai alfarma.
Ya ce: “Yawanci azumi ga dan Adam a doron kasa yana daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana a wani wuri da ke da faduwar rana ko fitowar rana cikin sa’o’i 24”. Amma idan mutum yana wurin da babu faɗuwar rana ko fitowar rana a cikin sa'o'i 24, muna yin wani abu da ake kira "calculation" wanda ke nufin lissafi.
Ya kara da cewa: Ana yin wannan aikin ne ta hanyar la'akari da sa'o'i 24 tare da raba shi daidai. Don haka ana raba lokaci zuwa sa'o'i 12 a rana da sa'o'i 12 na dare. Ana yin azumin sa'o'i 12, wanda ana daukar sa'ar farko a matsayin farkon sa'o'i 12 da kuma karshen sa'o'i 12 a matsayin lokacin buda baki da kuma sallar magriba.
Ya kuma jaddada cewa dan sama jannatin na iya cin abinci bayan karshen sa'a 12 kuma ya kamata a kirga lokacin na tsawon sa'o'i 12. Idan wani yana son yin azumi, wannan zagayowar tana maimaita kanta.
Manek ya ce: Ba a wajabta yin azumi a cikin tafiya ba kuma dan sama jannati na iya yin azumi bayan ya isa kasa.