IQNA

Kafa kasuwar Ramadan a Montreal, Canada

21:27 - March 21, 2023
Lambar Labari: 3488845
Tehran (IQNA) Yayin da watan Ramadan ke gabatowa, musulman kasar Canada suma suna shirye-shiryen gudanar da ayyukan wannan wata. Musulman birnin Montreal ma sun yi maraba da wannan wata mai alfarma ta hanyar kafa kasuwar bajekoli ta Ramadan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ‘City News’ cewa, ana ci gaba da shirye-shiryen gudanar da azumin watan Ramadan a birnin Montreal na kasar Canada. A wannan birni an taru a kasuwar hada-hadar kasuwanci da ke da alaka da bukatun watan. Kamfanin Azzdah Events Group ne ya shirya kasuwar, a yankin Karnak Shriners na Dollard-des-Ormeaux, da nufin tallafawa kasuwancin gida a cikin garin.

Wannan kasuwar ta hada da dillalai 27 da suka ba da kayayyaki kamar su tufafi da abinci na gida.

Amber Younes, jami’ar da ke kula da shirya kasuwar kasuwar Ramadan ta ce: A wannan kasuwar an samar da fili ta yadda jama’a za su rika tanadin bukatun watan Ramadan.

Ya kara da cewa: Muna bukatar abinci iri-iri; Ramadan lokaci ne na murna a gare mu kuma mun riga mun shirya don Ramadan.

Azzdah Events Group za ta karbi bakuncin wata kasuwar Ramadan a ranar 1 ga Afrilu (12 ga Afrilu).

Bisa kididdigar da aka yi a shekarar 2022 a kasar Canada, yawan musulmin kasar miliyan daya da dubu 150 ne.

 

4129202

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: ramadan birnin Montreal tufafi abinci musulmi
captcha