Musulmai na maraba da watan mai alfarma tare da gudanar da ayyuka daban-daban kamar kakkabe kura da tsaftace masallatai da wurare masu tsarki, yin ado da haskaka tituna, sayen sabbin tufafi, dafa abinci na musamman da kayan zaki, gudanar da shirye-shiryen karatun Alkur'ani, halartar sallolin jam'i da bayar da abinci ga musulmi a wurin taruka a lokacin buda baki.