Tehran (IQNA) Ofishin Ayatollah Sistani ya sanar da ra'ayinsa game da mai yiwuwa za a gudanar da sallar Idi.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ofishin Ayatollah Sistani mai kula da harkokin mabiya mazhabar Ahlul bait a birnin Najaf Ashraf ya fitar da wata sanarwa tare da bayyana ra’ayinsa dangane da lokacin da za a yi sallar Idi.
Don haka ana hasashen ranar Asabar mai zuwa za ta kasance daidai da 22 ga Afrilu, wato daya ga watan Shawwal da kuma Idin karamar Sallah.