IQNA

Nuna Wariya ga Musulmi da 'yan Afirka a Faransa

16:44 - May 04, 2023
Lambar Labari: 3489087
Tehran (IQNA) A cewar wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta wallafa, Musulmi da 'yan Afirka a Faransa na fuskantar ayyukan wariya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Al-Sharrooq ya bayar da rahoton cewa, hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wani rahoto kan halin da ake ciki na hakkin bakin haure daga kasashen Afirka da Larabawa da kuma iyalansu a kasar Faransa, inda ta bukaci mahukuntan Faransa da su dakatar da ayyukan da suke tauye hakkin wadannan mutane da kuma hakkinsu, da kuma daina kamfen na wariyar launin fata da kiyayya ga musulmi.

Hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga hukumomin Faransa da su bayar da garantin kare hakkokin ma'aikatan bakin haure ta hanyar kafa doka.

Rahoton na wannan majalisar ya bayyana cewa, har yanzu al'ummar Afirka na fuskantar wariya saboda launin fatar jikinsu, kuma hirarrakin da aka yi a kan haka ta tabbatar da hakan.

A saboda haka ne aka ba da shawarar a cikin wannan rahoto cewa, ya kamata Faransa ta zage damtse wajen yaki da laifuffuka da barazanar da ke haifar da yada kiyayya ta addini da abubuwa kamar kyamar Musulunci.

A cikin rahoton kwamitin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya, inda ya soki halin wariyar launin fata da jami'an tsaron Faransa ke yi da fursunonin, an bukaci daukar matakan tabbatar da bincike na nuna son kai daga cibiyoyin gwamnati a duk wani lamari na wariyar launin fata.

 

 

 

4138439

 

 

captcha