Lusaka, babban birnin kasar Zambiya, yana da masallatai da ke baje kolin kyawawan fasahohin addinin Musulunci. Wasu daga cikin wadannan masallatai sun hada da Lukman, Tauhidi da kuma Omar Al-Farooq, wadanda suke jan hankalin musulmi da dama a kowace rana a wannan kasa ta Afirka.