Kwadayi na daya daga cikin munanan halaye na dabi'u da Alkur'ani ya yi nuni da su kuma babban cikas ne ga ci gaban al'umma.
Kwadayi dabi'a ce da ke tilasta wa mutum tarawa fiye da bukatunsa, kuma yana daga cikin halaye masu halakarwa da bata tarbiyya.
Idan muna so mu bayyana kwadayi a cikin jumla guda, ita ce: mai kwadayi kullum yana cikin wahala kuma wahalarsa madawwamiya ce.
Rayuwar masu kwadayi tana cike da azaba da wahala domin ba su taba samun gamsuwa ba ko da duniyar tasu ce. Kullum suna ƙoƙarin karɓar kuɗi, amma ba za su taɓa jin daɗinsa ba. Kuma da yake duniya ba ta dawwama, kuma al’amarinsa a rufe yake da mutuwarsa, to, duk abin da aka tara za a je ga magadansa, ba zai xaukar wani abu da shi ba sai mayafi.
Amirul Muminin Ali (AS) yana cewa: Kwadayi shi ne tushen wahala ta har abada.
Ya zo a cikin aya ta 128 ta tuba: Lalle ne, haƙĩƙa wani Manzo daga cikinku yã je muku, wanda yake damuwa da wahalar da ku ka shiga, shĩ ne mai kwaɗayin (shiriyar) ku, kuma Mai tausayi ne ga mũminai.